BINCIKE: Ana fama da rashin tsaftaccen ruwa a Najeriya

0

Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA, hukumar kididdiga na kasa NBS da hukumar hana yaduwar cutar kanjamau na kasa NACA sun gano cewa akalla gida daya cikin gidaje uku basa iya samun tsaftatacen ruwa a Najeriya.

Binciken da wadannan hukumomi suka gudanar a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017 ya nuna cewa mutanen da basu iya samun tsaftatacen ruwa kan yi fama da cutar amai da zawo sanadiyyar kwayar cutar ‘Escherichia coli’ da ake yawo a irin wadannan ruwa.

” ita dai wannan kwayar cutar ‘Escherichia coli’ wajen kala uku take; akwai wanda bata cutar da mutum amma sauran biyun kuwa suna matukar cutar da lafiyar mutum domin sune suke dauke da cutar amai da zawo a jikin mutum.”

Binciken ya nuna cewa a shekarar 2011 adadin mutanen dake samun tsaftatacen ruwa a Najeriya sun kai 58.5, a shekarar 2012 kuwa sun dan ragu zuwa 57.8, a 2014 an Karu zuwa 62.2, a 2015 yawan ya Kai 69.6 bisa 100.

Duk da hakan binciken ya nuna cewa mutane 52.3 a yankin arewa maso gabashin kasar nan sun fi fama da rashin samun tsaftataen ruwa.

Bayan wannan bincike jami’ar hukumar UNICEF Maureen Zubie-Okolo take kira ga gwamnati da ta kafa kudirorin da zai taimaka wajen samar wa mutane tsaftataccen ruwa da muhalli domin haka zai taimaka wajen inganta lafiyar mutanen musamman na yara kanana sannan Kuma ya kare su da Kowa da Kowa daga kamuwa da cutar amai da zawo.

Share.

game da Author