Barayi 560 sun tuba a Jigawa

0

Gungun barayi 560 ne suka tuba daga sana’ar sata da fashi a taron gangami da suka hada a garin Kudai, wani kauyen Dutse, jihar Jigawa.

Ahmadu Dodo wanda shine shugaban kungiyar gyara kayanka a garin ya ce tubabbun barayin sun mika wuya ne suna masu yin nadama ga abubuwa da suka aikata a baya.

Dukkan wadanda suka tuba, sun roki yafiya sannan sun dauki alkawarin taimakawa wajen tona asirin duk wani barawo da yake sata ko fashi a kauyukan jigawa.

Daruruwan mutane ne daga kauyuka dabam-dabam suka halarci bukin.

Share.

game da Author