Ba kowa bane Allah ya yi wa baiwar da ya yi wa Buhari; Za mu lashe zaben 2019 – Tinubu

0

Jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya gana tare da Shugaba Muhammadu Buhari, mako daya bayan nada shi da aka yi ya sasanta rigingimin da ke tsakanin manyan jam’iyyar.

A ganawar da ya yi da gidan talbijin na NTA bayan fitowa daga wurin shugaban kasa, Tinubu ya bayyana cewa: “Ita dimokradiyya dama abu ce da ke tafiya kafada da kafada da kokarin sasanta rikici da rigingimun da ke dabaibaye da ita.

Ya kara da cewa ba za a iya gina dimokradiyya ba har sai an fahimci sabanin da ke tattare da ita, kuma an samo hanyoyin magance su.

Tinubu ya ziyarci fadar shugaban kasa tare da tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC, Bisi Akande, ya ce, umarni da Buhari ya ba shi na ya sasanta bambance-bambancen da ke cikin jam’iyya mai mulki, shi ne abu mafi alheri wajen inganta dimokradiyya a Najeriya.

“Samun irin su Buhari a Afrika a yanzu ba su da yawa. Mutum ne da ya yi soja, ya yi shugaban kasa na soja, kuma kafin nan da shi aka yi yakin Basasa. Sannan kuma ga shi ya shiga cikin dimokradiyya ya na bada gudummawarsa ta wajen kyakkyawan shugabanci da ya ke aiwatarwa.”

Dangane da zaben 2019, Tinubu ya ce APC ta fi sauran jam’iyyun kasar nan samun haske da alamomin samun nasarar zaben. Don haka ya ce, “Mu za mu lashe zaben 2019.”

Da ya juya kan tsoffin shugabanni Ibrahim Babangida da Olusegun Obasanjo, wadanda su ka rubuta wa Shugaba Buhari wasika suka shawarce shi kada ya tsaya takara a 2019, Tinubu ya ce ai shi idan ya raina kasuwa, to ko sautu ba ya yi a cikin ta.

Sai ya ce wadannan tsoffin shugabannin sun yi ta su rawar, sun gama, kuma sun kai gargara, ya kamata su janye gefe su bar Najeriya ta ci gaba a hannun masu kishin da za su kara inganta ta.

Share.

game da Author