ARTABU A ZAMFARA: Yadda ‘Yan Sanda suka ritsa masu garkuwa da mutane

0

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Zamfara ta bayyana nasarar kashe wani rikakken mai garkuwa da mutane a lokacin da shi da tawagar sa suka kai hari a kauyukan ‘Yartasha da Ruwan-gizo, suka sace wani Bilyaminu Abdullahi.

Kwamishinan ‘Yan sanda Kenneth Embrimson, ya ce sun samu labarin maharan sun isa kauyukan har sun yi awon gaba da Bilyaminu, amma su ka yi nasarar yi musu kwanton-bauna, inda suka bude musu wuta.

Ya ce an kashe gogarman masu garkuwa da mutanen an kuma kama wasu takwas, yayin da wasu kuma suka gudu da harbin bindiga a jikin su.

Ya kuma tabbatar da cewa sun samu nasarar ceto Bilyaminu daga maharan da suka so tserewa da shi. Sannan kuma an samu bindigogi kirar AK47 guda biyu, albarusai 75 da kuma Babura biyu a hannun su.

Ebrimson ya gabatar da gawar gogarman mai garkuwar a gaban manema labarai a Gusau.

Bayan wannan, kwamishinan ya kara da cewa a ranar Asabar ma an kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kauyukan Daraga da Dankurmi a cikin Karamar hukumar Maru.

Kuma an same su da bindigogi kirar gargajiya da harsasai.

Kwana daya kuma kafin wannan, ya ce an cafke wasu masu garkuwa da mutane har su biyar a garuruwan Kabala da Yangaladima cikin Kananan Hukumomin Maradun da Maru duk a cikin jihar Zamfara. An kuma kama wasu a Magarya cikin Karamar Hukumar Zurmi.

A karshe ya ce an cafke wani dillalin bindigogi ga masu garkuwa da mutane, kuma shi ake kai wa kudaden fansa idan an yi garkuwa da mutane.

Kwamishinan ‘Yan sanda ya ce an samu tsabar kudi har naira miliyan 2.6 a hannun sa, sannan kuma an samu kudin Sefa ta Nijar kuda 21 duk a hannun sa.

Ya roki jama’a su rika kai rahotannin duk wasu da ba su amince da gilmawar su ba da gaggawa.

Share.

game da Author