Tsohon Gwamnan Jihar Lagos, Bola Tinubu, ya nuna damuwa dangane da zargin da ya yi cewa shugaban jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun ya yi masa yankan-baya a kokarin da Tinubu din ya ke yi na sasanta rikice-rikicen da suka dabaibaye APC.
Tinubu ya rubuta takarda a ranar Laraba cewa duk da tabbacin da Oyegun ya ba shi na bayar da hadin kai a shawo kan rigingimun da suka dabaibaye APC, amma ya gano cewa ya na yi wa kokarin da ya ke yi kafar-ungulu.
Sai dai kuma APC ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba ta da wani abu da za ta ce dangane da wasikar da Tinubu ya aika wa Oyegun a jiya Alhamis.
A ranar Laraba 21 Ga Fabrairu ne Tinubu ya aika wa Oyegun da wasikar, kuma ya tura kwafen ta ga Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara.
ABIN DA WASIKAR TA KUNSA
” Rai na ya baci matuka dangane da yadda na gano irin shantale min kafafuwa da ka ke yi, domin kada na samu nasarar aikin sasanta rigingimun APC, wanda Shagaba Muhammdu Buhari ya ba ni. Duk kuwa da cewa tun farko ka ba ni tabbacin cewa za ka bada hadin kai domin a shawo kan matsalolin.”
Tinubu ya ce ya tuna yadda Oyegun ya kara nanata masa jihohin da rigingimun su ka fi muni, kamar Kogi, Kano, Adamawa da Kaduna. Ya ce amma maimakon Oyegun din a matsayin sa na shugaban jam’iyya ya hada kai a magance su, sai ma makarkashiya ya ke ta kullawa don kada Tinubu ya yi nasara.
Tinubu ya buga misali da yadda Oyegun ya halarci bikin bude ofishin daya bangare na jihar Kogi, bayan kuma tun tuni akwai ofishin jam’iyyar na jiha.
Tinubu ya gargadi Oyegun da ya daina kitsa kulle-kullen da zai kara rura wutar wargaza jam’iyya.
Idan ba a manta ba, cikin 2016 Tinubu ya nemi Oyegun da ya sauka daga shugabancin APC.
Ya zuwa yanzu dai sakataren APC Bolaji Abdullahi ya ki ce wa PREMIUM TIMES komai, yayin da shi kuma Tinubu ya nemi Oyegun da ya damka masa rahotannin halin da ofisoshin jam’iyyar na jihohi ya ke ciki.