APC ta kafa kwamitin duba rigingimun Kaduna

0

Jam’iyyar APC mai mulki ta kafa kwamitin mutane uku da za su duba rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a cikin jihar Kaduna, wanda har ya kai ga an sa katafila an rushe ginin ofishin bangaren da ba su tare da gwamna Nasir El-Rufai.

An dai rushe ofishin ne mai lamba 11b, da ke kan titin Sambo Road, Kaduna.

Jiya Alhanis ne Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar APC, Bolaji Abdullahi ya bayyana haka, biyo bayan rushe ginin da aka yi wanda mallakar Sanata Sulaiman Hunkuyi ne.

APC ta ce za a duba yadda asalin sabanin ya ke har ta kai ga rushe ginin.

Kwamitin na mutane uku na karkashin Mataimakin Shugaban Jam’iyya ne shiyyar Kudu, Segun Oni, sai George Moghalu da kuma shugabar mata Rakiya Aliyu.

Share.

game da Author