An tsincin gawar wata mata a rijiya bayan fasto ya gama yi mata addu’a

0

Hankalin mabiyar darikar Cherubim da Seraphim ya tashi bayan da aka tsinci gawar wata mata a cikinn rijiyar da ke harabar cocin su a unguwar Ayedun da ke cikin garin Akure, babban birnin jihar Ondo.

Matar mai suna Funke Ojo, an tsinci gawar ta ne bayan da wasu suka je za su debi ruwa a jiya Lahadi. Wasu sun ce lafiya kalau matar ta ke kafin ta rasu, amma kwana daya kafin a tsince ta, an tabbatar da cewa mahaifiyar ta ta kai ta a gaban fasto mai rike da cocin domin ya yi mata addu’a kan wani abu da ke damun ta,

An shaida wa PREMIUM TIMES cewa bayan da fasto ya gama yi mata addu’a, sai ta yanke shawarar za ta kwana a cocin, ita kuma mahaifiyar ta, ta koma gida.

Bayan da matasa suka ciro gawar Funke daga rijiya domin a binne ta, su kuma jami’an ‘yan sanda sun cafke fasto Segun Oriade, ya na hedikwatar su ta jihar Ondo.

Sun tabbatar da cewa su na bincike ne, domin har ta rigaya ta koma gida, amma daga baya ta koma cocin da nufin za ta kwana a can.

Share.

game da Author