Ministan Abuja Muhammad Bello ya sanar da rage tsawon dokar hana walwala da aka saka a garin Bwari sanadiyyar yamutsi da akayi tsakanin mazauna garin a shekarar 2017.
Ministan ya sanar da sassauta dokar hana walwala daga karfe 6 na yamma – 6 na safe zuwa karfe 10 na yamma – 5 na safe.
Ya kara da cewa gwamnati ta yi haka ne ganin cewa an sami zaman lafiya a garin na Bwari.
Shugaban karamar hukumar Bwari Musa Diko ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara tsananta tsaro.