An rufe Jami’ar Modibbo Adama, Yola

0

A yau Litini hukumar jami’ar Modibbo Adama dake Yola ta sanar da rufe makarantar sai saboda rikici da ya kaure tsakanin daliban jami’ar.

” Sakamakon barkewar rikici a jami’ar da yayi sanadiyyar mutuwar wani dalibi, hukumar makarantar na kira ga dalibai da su tattara komatsansu su fice da ga jami’ar.” Sanarwan hukumar makarantar.

PREMIUM TIMES ta jiyo daga wata majiya cewa rikicin ya samo asali ne tun bayan zaben shugabannin kungiyar dalibai da zargin wani dalibi da akayi wai yayi rubutun batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) a shafinsa na WhatsApp.

Daga nan ne fa rikici ya barke inda akayi kone-kone da doke-doke tsakanin daliban makarantar.

Hukumar makarantar ta rufe jami’ar daga yau Litini.

Share.

game da Author