Hukumar NAFDAC ta rufe gidajen buredi 24 da suke aiki ba tare da lasisi ba a Maduguri, jihar Barno.
Jami’in hukumar Nasir Mato ya sanar da haka wa manema labarai yau Laraba inda ya kara da cewa sun yi haka ne saboda karya dokar kafa masana’antu da hukumar ta kafa da masu wadannan gidajen buredi suka yi.
” Rashin tsaftace kayan aiki da wurin aiki sannan da rashin yin rajista da hukumar mu na daga ciki dalilan da ya sa muka rufe wadannan gidajen buredi.”
Discussion about this post