An kori malamai 747 a jihar Filato

0

Shugaban Hukumar Bayar da Ilmi a Matakin Farko, UBE, na jihar Filato, Mathew Sule, ya bayyana cewa an kori malaman makaranta 747 a jihar.

Ya ce wadanda korar ta shafa, sun kasa kawo satifiket din da zai nuna cewa sun cancanci zama malaman makaranta.

Sule ya kara da cewa har ila yau kuma an yi ritaya ga dukkan wanda ya kai shekarun a yi masa ritaya.

Dangane da wasu malamai 141 da aka sake maidawa, Sule ya ce an dawo da su ne saboda su na da takardar shaidar cancanta su yi koyarwa.

Gwamnatn da ta gabata ta Gwamna Jonah Jang, kafin ta sauka sai da ta kori malaman firamare dubu 4000, wadanda ta ce ta bincika ta gano ba su cancanta ba.

Sule ya ce a yanzu akwai bukatar daukar wasu kwararrun malaman domin a cike gurabu yadda za a samu wadatattun malamai da za su dauki kowane darussa.

Share.

game da Author