Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta sanar cewa wasu matasa a tashar mota dake jihar sun kashe wasu Fulani makiyaya bakwai da ke hanyar su ta zuwa garin Okene daga Jalingo.
Su dai Fulanin sun yada zango ne a tashar motar dake Gboko kafin su ci gaba da tafiyar su, in da ashe sun tsaya wa ajalin su ne. Kafin su ankara wasu matasa dauke da makamai suka far musu suka kashe su a tashar.
Kakakin rundunar Joel Yamu Moses ya bayyana cewa matasan sun kai wa wadannan Fulani hari ne da misalin karfe 9:30 na safe a Gboko ranar Laraba.
Ya ce bisa ga binciken da suka gudanar wadannan Fulanin sun shiga mota ne daga Jalingo zuwa Okene jihar Kogi inda shi direban motar ya ya da zango a wannan tasha domin su dan huta.
Bayan haka gwamnan jihar Samuel Ortom da kwamishinan ‘yan sandan jihar Fatai Owoseni sun ziyar ci tashan sannan sun sanar da kama wasu mutane da ake zargin su ne.
” Muna tabbatar muku da cewa za mu hukunta duk wadanda samu yana da hannu wajen aikata wannan mummunar aiki.”
Sannan Ortom ya kafa dokar hana walwala a Gboko domin shawo kan matsalar.
Daga karshe shugaban kungiyar makiyaya ‘Miyetti Allah’ na yankin Arewa Maso Gabas Mafindi Danburam yace suna da masaniyyar harin da aka kai wa ‘yan uwansu a wannan tashar.
Ya ce yana kira ga gwamnati da ta hukunta wadannan mutane.