An kama masu garkuwa da mutane a Jihar Zamfara

0

Rundunar ‘yan sandar jihar Zamfara ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da sace mutane a kauyen Dankadon-Daji dake karamar hukumar Talatan-Mafara.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kenneth Embrimson ne ya sanar da haka wa manema labarai a Gusau ranar Litini inda ya kara da cewa sun kama wadannan mutane ne ranar 18 ga watan Faburilu bayan rundunar ta sami labarin cewa mutanen sun aika wa mazaunan kauyen Dankadon-Daji da wasikar barazanar sace mutanen garin idan har basu tara musu kudi sun aika musu ba.

” Da jin haka sai muka fara fakon su inda muka sami nasarar kama su a daidai suna kokarin karban Naira 39,500 daga wajen mazauna wannan kauyen.”

Emgrinson ya ce za su kai mutanen kotu da zaran sun kammala bincike a kai.

Share.

game da Author