An kama likita mai siyar da Jarirai a Abuja

0

Hukumar NAPTIP ta tona asirin wani likita da ta kama ya na siyar da jarirai a asibitin sa dake unguwar Nyanya dake Abuja.

Kakakin hukumar Josiah Emerole da ya sanar da haka ya ce sun kama shugaban asibitin ‘Akuchi Herbal Concept’ da laifin siyar da jarirai ga matan da basu iya haihuwa.

Emerole ya kara da cewa wannan likita yakan shirya ne da mata wadanda basu haihuwa sai ya ce musu suna da ciki, indda bayan watanni tara sai su dawo asibitin su biyashi ya basu sabon jariri kamar su ne suka haifa.

Sukan yi ciniki ne sosai sannan su biya shi kudi masu yawa.

Share.

game da Author