An kama dan Boko Haram a harabar NTA dake Jihar Edo

0

Jami’an tsaro na ‘Civil Defence Corps (NSCDC) reshen jihar Edo sun bayyana cewa ma’aikatan sun sun kama wani dan Boko Haram da yake ta gararamba a harabar gidan Talabijin na kasa, NTA reshen Jihar.

Jami’in hukumar Makinde Ayinla ya ce sun kama dan Boko Haram din mai suna Sani da asubahin ranar Asabar.

“Tun daga karfe biyu na dare zuwa hudu na safe ma’aikatan mu suka hango Sani na gararamba a harabar ma’aikatar wanda hakan ya sa suka gaggauta kama shi.”

Ayinla ya ce yayin da suke gudanar da bincike Sani ya fada musu cewa ya sharara ne a kisa, garkuwa, siyar da gabobin jikin mututane da fashi da makami a kungiyar Boko Haram din.

Sani yace kungiyar su na amfanin da da manyan makamai amma ba zai iya kai jami’an tsaron mabuyar kungiyar ba.

” Allah kadai ne zai iya kai mu mabuyan.”

Ayinla ya ce sun mika Sani ga hukumar SSS domin ci gaba da bincike.

Share.

game da Author