An horas da masu yi wa kasa hidima 1,500 sana’o’in hannu a Sokoto

0

Shugaban hukumar kula da aiyukan masu yi wa kasa hidima na jihar Sokoto NYSC Musa Abubakar ya bayyana cewa jihar ta horas da masu yi wa kasa hidima 1,500 sana’o’in hannu a sansanin Wamakko dake jihar.

Ya fadi haka ne ranar juma’a yayin da ya kai ziyarar gani wa ido kayan da masu yi wa kasa hidima suka sarrafa daga darasoshin da suka koya.

” Mun horas da masu bautar kasa da aka turo jihohin Sokoto, Kebbi da zamfara sana’o’i kamar su kiwata dabobbi, sarrafa sabulu da manshafawa, daukar hota, saka, dinki da sauran su a sansanin Wamakko’’.

Abubakar ya ce sun hada hannu da babban bankin Najeriya, Bankin Heritage,da sauran su wajen samar wa matasan kayan aiki.

Share.

game da Author