Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Geidam ya sanar cewa Gwamnatin sa ta dauki ma’aikatan kiwon lafiya 63 a sabuwar jami’ar jihar.
Kakakin gwamnan Abdullahi Bego ya bayyana haka ranar litini inda ya kara da cewa ma’aikatan da aka dauka aiki sun hada da malamai ne da wadanda ba malamai ba.
Ya ce aikin nadu na dindin din ne, sannan za a biya su fansho idan suka yi ritaya da Hutu.
A karshe Bego ya kuma ce za a ba su horo kafin su fara aiki.