An dage taron Majalisar Zartaswa na ranar Laraba

0

Majalisar Zartaswa ta dage taron ta na mako-mako na ranar Laraba, da ta ke gudanarwa a Fadar Shugaban Kasa, a kowace Laraba.

Taron na wannan makon an dage shi ne saboda Shugaba Muhammadu Buhari da wasu ministoci da dama su samu damar halartar wani taro na kasa-da-kasa da za a gudanar a zauren taro da otal din Hilton.

Taron dai ya danganci batutuwa ne kan Tafkin Chadi, kamar yadda Fadar Shugaban Kasa ta yi sanarwa.

Share.

game da Author