An bude asibiti don kula da lafiyar mata da aka yi musu fyade a jihar Barno

0

Gwamnatin jihar Barno tare da hadin guiwar kungiyar kasashen Turai EU sun bude asibitin kula da wadanda aka yi wa fyade a jihar.

Uwar gidan gwamnan jihar Nana Shettima wacce ta kadamar da asibitin ranar Litini a cikin babbar asibitin Umaru Shehu a Maiduguri ta ce ‘faduwace ta zo dai dai da zama’ da aka gina asibiti na musamman ganin yadda yi wa ‘yan mata da mata fyade ya zama ruwan dare a jihar saboda fama da akayi da aiyukan Boko Haram.

” Ya zama dole a hada hannu don ganin cewa an kawar da wannan mummunar abu da ta kutso kai a cikin al’umar mu.”

An bude asibiti don kula da lafiyar mata da aka yi musu fyade a jihar Barno

Bayan haka kwamishinan ‘yan sandan jihar Damian Chukwu a nashi tsokacin ya ce jihar Barno na daya daga cikin jihohi a kasar nan da fyade ya zamo ruwan dare.

Daga karshe shugaban gudanarwa na wannan asibitin Tabiu Mohammed yace asibitin za ta yi aiki da rundunar ‘yan sanda, ma’aikatar harkokin mata da ci gaban yara, ma’aikatar shari’a, don ganin sun kawar da wannan annoba a jihar.

Share.

game da Author