Wani magidanci mai suna Ola ya roki kotu dake Igando jihar Legas da ta raba auren sa da matar sa saboda kwana da wasu mazan da ta keyi.
Ola dai dan shekara 34 sannan ya bayyana wa kotu cewa matar sa Aminat na dauke da cikin da ba na shi ba sannan ya na tabbatar wa kotu cewa ita matar sa tsafi ta ke yi.
” Dalilin zama da wannan mata duk na rasa komai nawa inda gashi na wayi gari ba ni da komai, hatta abinci ma sai na roka.”
Ya kuma kara da cewa Aminat bata bashi girma a matsayin sa na mijin ta domin ba zai iya hanata ba ko ya saka ta wani abu.
Saboda wadannan hujjoji da ya zayyano ne ya roki kotu ta raba auren sa da Aminat ko ya dan samu ya sarara.
Duk da wannan korafe- korafe da Ola ya zayyano wa Kotu, da aka nemi ji daga bakin Aminat, ta karyata mijin nata, cewa shine ke kwana da mata a waje sannan shine matsafi.
Ko da yake Amina mai shekaru 24 ta amince cewa lallai tayi masa barazanar kashe shi, amma tayi haka ne don ta kare kanta domin shine yafara yi mata irin wannan barazana.
” Tun kafin muyi aure, Ola yayi mini alkawarin biya mini kudin makaranta domin in ci gaba da karatu bayan mun yi aure, sai gashi bayan auren yaki yin haka sai ya buge da biya min kudin koyan dinki. Ina rokon kotu ta raba auren kawai.” Inji Aminat.
Sai dai kuma dukkan su basu sami yadda suke so ba domin Alkalin Kotun Akin Akinniyi kira ya yi ga ma’auratan da su koma su sasanta kan su sannan ya daga ci gaba da zaman shari’ar zuwa watan Maris.
Discussion about this post