Allah ya yi wa fitaccen dan jarida, Mahmoon Baba-Ahmed ya rasuwa

0

Allah yayi wa fitaccen dan jarida, Mahmoon Baba-Ahmed rasuwa a daren Juma’a a Kaduna.

Mahmoon wanda wa ne ga Shugaban ma’aikatan ofishin shugaban Majalisa Sanata Bukola Saraki, Dr Hakeem Baba Ahmed, da Datti Baba Ahmedfitaccen ne wajen yin fashin baki ga siyasar Najeriya a tashoshin talabijin na DITV da Liberty dake Kaduna.

Kamar yadda Dr Hakeem ya sanar a shafin sa na Facebook, za ayi wa marigayi Mahmoon sallah a masallaci Sultan Bello, bayan sallar Juma’a, a Kaduna.

Allah Ya ji kan sa, Amin.

Share.

game da Author