Ali Nuhu da Adam Zango sun Shirya

0

Bayan watanni da aka diba ana ga maciji tsakanin jaruman Kannywood Adam Zango da Ali Nuhu, ya kawo karshe bayan sasanta su da akayi.

Idan ba a manta ba Ali Nuhu da Zango sun sa fadawa turmutsitsin rashin jituwa da sanadiyyar haka yakan jawo su yi baram baram, kowa baya wa wani magana har na dan tsawon wani Lokaci.

Irin haka ya taba faruwa a 2015, inda jaruma Rahama Sadau ta zargi Adam Zango da neman sai ya kwana da ita kafin ya saka ta a fim din sa mai suna Duniya makaranta. Hakan yajawo mummunar sabani tsakanin Rahama da Adamu inda daga baya ta fito kuru-kuru ta nemi gafarar abin da ta ce.

Shima Adamu a wannan lokaci ya roketa yafeya game da abin da ya faru. Wannan rigima dai ya sa sun dan ja iska da Ali Nuhu ganin cewa shine uban gidan ita Rahama.

Daga baya sun shirya.

A wannan karon, abinda ya hada su bai wuce ‘yan kai gukma ba, kamar yadda wani ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa wai an dauki maganar Ali ne aka kai wa Zango, shi kuma ya fusata ya yi wa Ali wasika barambaram.

Yanzu dai kome ya washe bayan shin manya maganar, an warware rikicin jaruman sun yayyafe an ci gaba da gashi.

Share.

game da Author