ALHAMDULILLAH: An sako wanda aka kashe mahaifin sa, aka kama wai dan Boko Haram ne a Kano

0

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAH WA BARA KA TUHU

DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH, MAI KOWA MAI KOMAI, MAI KASHEWA MAI RAYAWA, DA YA AZURTA MU DA SAMUN SHUGABANNI MASU SAURARON KOKE-KOKEN TALAKAWAN SU.

YA ALLAH MUN GODE MAKA A KAN WANNAN BAIWA DA NI’IMA DA KAYI MUNA. YA ALLAH KA KARA TAIMAKON KA A KAN WADANNAN SHUGABANNI, AMIN.

YA KU ‘YAN UWA NA MASU DARAJA, MASU GIRMA, IDAN BAKU MANTA BA, A ‘YAN KWANAKIN NAN, NAYI WANI BAYANI GAME DA ZALUNTAR WANI BAWAN ALLAH, WATO MARIGAYI MUHAMMAD INUWA MAI KAJI GAYAWA DA JAMI’AN TSARO SUKA YI, A INDA SUKA HARBE SHI, SUKA KASHE SHI HAR LAHIRA, HAKA SIDDAN, BAI SAN HAWA BA, BAI SAN SAUKA BA, BABU LAIFIN ZAUNE BABU NA TSAYE, A KANO. SANNAN BAYAN SUN KASHE SHI SAI SUKA KAMA DAN SA ABUBAKAR SUKA TSARE SHI, WAI SUNA ZARGIN CEWA SHI DAN BOKO HARAM NE. WANDA KOWA YASAN DA CEWA SUN YI HAKAN NE DOMIN SU KARE KAN SU GAME DA WANNAN AIKA-AIKA DA SUKA YI.

ALHAMDULILLAH, ALLAH SUBHANAHU WA TA’ALA YA ALBARKACI WANNAN BAYANI NAWA, A INDA HAR YA TAFI INDA AKE BUKATA, YA KAI KUNNEN SHUGABANNI. SANADIYYAR YADUWAR SA A KAFAFEN YADA LABARAI IRIN SU PREMIUM TIMES HAUSA, DA FACEBOOK DA WHATSAPP DA SAURAN SU.

SANNAN SASHEN HAUSA NA MURYAR AMURKA (VOA HAUSA) SUN DAGE KWARAI, KUMA SUN YI KOKARI MATUKA WAJEN BAYYANAR DA WANNAN ZALUNCI. ALLAH YA SAKA MASU DA ALKHAIRI, SU DA DUKKANIN MA’AIKATAN SU, AMIN.

BAYAN NAYI BAYANI NE, KUMA ALHAMDULILLAH, ALLAH YA YADA SHI, SAI MAI MARTABA ADALIN SARKI, SARKIN KANO, MUHAMMADU SANUSI NA II YA TAMBAYE NI, SHIN MEYE SUNAN WANNAN MUTUM DA WANNAN ABU YA FARU DA SHI, SANNAN A WACE ANGUWA YAKE A KANO? KUMA WALLAHI, MAI MARTABA SARKI YA TAMBAYE NI NE TSAKANINSA DA ALLAH, BA DOMIN KOMAI BA ILLA DA NUFIN DAUKAR MATAKIN YIN ADALCI GA IYALAN WANNAN BAWAN ALLAH. KUMA ALHAMDULILLAH, YANZU DAI DA SA BAKIN MAI MARTABA SARKI MUHAMMADU SANUSI NA II, DA KUMA SA BAKIN MAI GIRMA GWAMNAN JAHAR KANO, ALHAJI ABDULLAHI UMAR GANDUJE, ALLAH YA KADDARI AN SAKI WANNAN YARO ABUBAKAR DA AKA KAMA DA ZARGIN CEWA SHI DAN BOKO HARAM NE. MUNA GODIYA MATUKA A KAN WADANNAN SHUGABANNI NAMU, DA DUKKANIN WADANDA SUKA BADA GUDUMMAWA A KAN TABBATUWAR ADALCI A CIKIN WANNAN AL’AMARI. MUN GODE, MUN GODE, MUN GODE. ALLAH YA KARA GIRMA, DARAJA, JURIYA, HAKURI, TAWADU’U DA IMANI, AMIN.

YA KU ‘YAN UWA MASU ALBARKA, SAI DAI WANI HANZARI BA GUDU BA. BAYAN SAKIN WANNAN YARO ABUBAKAR DA AKAYI, YANZU ABUBUWA GUDA BIYU NE SUKA RAGE. NA FARKO: HUKUNTA JAMI’AN TSARON DA SUKA YI WANNAN AIKA-AIKA NA KISAN WANNAN BAWAN ALLAH, DA KWATO WA IYALAN SA HAKKIN SU. NA BIYU: TALLAFAWA IYALAN WANNAN BAWAN ALLAH, WATO IYALAN MARIGAYI MUHAMMADU INUWA MAI KAJI GAYAWA, KANO. DOMIN A SANI NA DA WANNAN MUTUM, SHI MAI YAWAN IYALI NE, MAI KOKARIN NEMAN HALAL DIN SA. SANNAN SHINE MAI NEMO MASU ABINDA ZA SU CI. YANZU AN KASHE SHI, KOMAI NASU KENAN YA TSAYA CAK! SANNAN SHINE YAKE DAUKE DA KARATUN ‘YA ‘YAN SA. YANZU TUN DA AN KASHE SHI, YAYA LABARIN KARATUN ‘YA ‘YAN NASA? SHIN ZA SU CI GABA DA KARATUN SU NE KAMAR ‘YA ‘YAN KOWA, KO KISAN MAHAIFIN NASU DA JAMI’AN TSARO SUKA YI ZAI KAWO KARSHEN KARATUN NASU? KAI, KAI, KAI, INA SAM! NASAN DA IKON ALLAH WANNAN BA ZAI FARU BA, TUN DA NASAN DA CEWA, MUNA DA ADALIN SARKI, MAI SAURARON KOKEN JAMA’AH, MAI TAIMAKON TALAKAWAN SA, KUMA MUJAHIDI. WANDA WALLAHI NI SHAIDA NE A KAN HAKAN, KUMA KO A GABAN ALLAH ZAN BAYAR DA SHAIDAR HAKAN. SANNAN KUMA GAMU DA GWAMNA ABDULLAHI UMAR GANDUJE, KHADIMUL ISLAM, MAI SAURARON KUKAN JAMA’AH.

YA KU JAMA’AH, KAR KU ZARGE NI DA BANBADANCI, KO GOYON BAYAN WANI DAN SIYASA. KUN SANNI SARAI, BANA BANBADANCI, SANNAN HAR KULLUN, NI, DA KARFIN IKON ALLAH, ZAN GOYI BAYAN GASKIYA NE KOMAI DACIN TA. SANNAN ITA GASKIYAR, DOLE NE A FADE TA KO A KAN WAYE. SANNAN MALAM BAHAUSHE YACE: YABON GWANI YA ZAMA DOLE.

KUMA WALLAHI, WALLAHI, WALLAHI, MU SANI, ALLAH YA AZURTA MU DA SARAKUNA MASU ADALCI DA TAWADU’U. ALLAH SHINE SHAIDA, BABU LOKACIN DA ZAMU SHAIDA WA MAI ALFARMA SARKIN MUSULMI (SULTAN) DA MAI MARTABA SARKIN KANO WATA DAMUWA DA KE DAMUN MUSULUNCI KO MUSULMI, FACE SUN SAURARE MU, KUMA SUN YI KOKARI WAJEN DAUKAR MATAKIN DA YA DACE. ALLAH NE SHAIDA A KAN HAKAN.

INA ROKON ALLAH YA KARA MASU DARAJA, DAUKAKA, DA NISAN KWANA, YAYI MASU SAKAMAKO DA GIDAN ALJANNAH FIRDAWS, AMIN.

SANNAN DON ALLAH, DON ALLAH, DON ALLAH, INA ROKON, AYI WA IYALAN WANNAN BAWAN ALLAH ADALCI, A KUMA TAIMAKA MASU. DOMIN BREADWINNER DIN SU SHINE MAHAIFIN NASU, KUMA YANZU AN KASHE SHI. DON ALLAH KAR WANNAN YA JAWO TAGAYYARAR WADANNAN BAYIN ALLAH. WATO IYALAN MARIGAYI MALLAM MUHAMMADU INUWA MAI KAJI GAYAWA, KANO.

ALLAH YA TAIMAKA, YA BADA IKON TSAYAR DA ADALCI, KUMA YA BADA IKON TAIMAKAWA, AMIN THUMMAH AMIN.

Wassalamu Alaikum,

NAGODE, DAN UWAN KU, MAI KAUNAR KU, MAI BIYAYYA A GARE KU HAR KULLUN:

Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Nigeria. +2348038289761.

Share.

game da Author