Akwai maganin kawar da matsanancin Damuwa – Likita

0

Wani kwararren likita dake zaune a kasar Britaniya, Landan Andrea Cipriani ya bayyana cewa mutane su daina yayada cewa wai mutumin da ya fada cikin matsanancin damuwa ba zai iya samun taimako daga likitoci ba.

Likita Andrea ya fadi cewa lallai akwai kwayoyi da mai fama da haka zai iya hadiya domin samun sauki da damuwar sa.

” Anyi gwaji kan wasu magunguna dabam dabam guda har 21 domin samun tabbacin ko za su iya taimakawa wajen samawa mai fama da matsanancin damuwa sauki. Kuma an samu nasara akai.”

Dalilin haka likitan ya roki mutane da su daina fadin wai ba a samun taimako don samar wa wanda ya fada irin wannan hali sauki ta hanyar asibiti.

Ya roki mutane da su watsar da irin wadannan camfe-camfe da akeyi da kan kawo rudani ga lafiyar jama’a.

Share.

game da Author