A yau Laraba wasu ‘yan uwan wani magidanci dake saida da abincin kaji a garin Daddara karamar hukumar Jibia jihar Katsina sun koka wa PREMIUM TIMES yadda harbin tsautsayi da wasu ma’aikatan kwastam dake aiki a yankin suka yi ta kashe dan su mai suna Amiru Abdulaziz.
Wani dan uwan mamacin Mallam Bello ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa harsashin ta sami dan uwan su ne a daidai ya fito shagon sa da yake siyar da abincin kaji ranar Talata da misalin karfe 5:30 na yamma.
” A ranar Talata da misalin karfe 5:30 na yamma wasu ma’aikatan kwastam sun biyo wasu masu fasakwaurin shinkafa suka yi harbi, harsashin bai tsaya ko-ina- ba sai a jikin dan uwan mu Abdu-Aziz inda nan take kuwa tayi ajalin sa”
Bayan haka ya koka da yadda ma’aikatan kwastamke kashe musu mutane cewa wannan ba shi ne karo na frako ba.
AbdulAziz ya bar mata daya da ciki da ‘ya’ya biyu.
Discussion about this post