Asusun samar da tallafi ga kananan kula na majalisan dinkin duniya UNICEF ta bayyana cewa adadin yawan yaran dake fama da matsanacin yuwan a Najeriya musamman ‘yan kasa da shekara biyar ya karu.
Jami’ar hukumar Maureen Zubie-Okolo ce ta sanar da haka a taron samun madafa game da wannan matsalar a Najeriya da aka yi a Enugu.
Okolo ta ce bisa ga binciken da hukumar gudanar da bincike na MICS ta gudanar a shekarar 2017 a gidaje 33,901 a jihohin kasar nan ya nuna cewa yaran dake fama da rama saboda yunwa ya karu daga kashi 24.2 zuwa 31.5 bisa 100, yaran da yunwa ya hana su girma sun karu suma daga kashi 34.8 zuwa 43.6 bisa 100 sannan adadin yaran da yunwa ke yin ajalin su ya karu daga kashi 10.2 zuwa 10.8.