A daina Zargin mu kan Zaben Kano – Hukumar Zabe ta Kasa

0

Hukumar Zabe ta Kasa ta roki jama’a da su daina dora mata laifi kan abin da ya faru a zaben kananan hukumomin jihar Kano da akayi a makon da ya gabata.

Kungiyoyin Sa-ido guda biyu da suka kula da yadda aka gudanar da zaben kananan hukumomi a Kano, wato ‘Centre for Informaion Technology, (CITAD) da Action Aid International Nigeria’,sun bayyana cewa yara kanana ne suka yi zabe a wannan zabe.

“Baya ga kananan yara da suka rika jefa kuri’a, an samu karancin kayan aiki, da karancin kuri’u. akwai wurin ma da kuri’a 200 kacal aka kai, amma kuma masu dangwala kuri’a sun haura 600.” Inji Hamza Usman,shugaban kungiyar CITAD.

Hukumar Zabe ta bayyana cewa zaben kananan hukumomi ba a hurumin ta ya ke ba saboda haka a yi mata uzuri a nan.

” Jihohi ke da iko kan hukumomin zabe a jihohin su, ba mu ba, saboda haka korafe-korafen da ake tayi na kananan yara sun yi zabe da murdiya da aringizo da aka ce an yi sakaci ne na hukumar zabe na jihar.

” Mu namu mu shirya zaben kasa ne, amma abinda ya faru ba mu da ta cewa akai domin abune da ya shafi jihohi. Kuma Idan ba a manta ba a ko ina akayi irin wannan zabuka,za ka ga gwamnati mai ci a Jihar ne ta lashe kujerun kaf.” Inji Oluwole Uzzi.

Ya bada misali da jihohi kamar su Akwa-Ibom, Osun, Kwara, Ekiti, da sauran su inda duka kujerun jam’iyyar gwamnati mai ci a jihohin ne suka lashe zabukan.

Share.

game da Author