‘Yan kunar bakin wake sun tada bam a Kasuwar Kifi, Jihar Barno

0

Wasu ‘yan kunar bakin wake su uku sun tada bam dake daure a jikin su a kauyen Kasuwan Kifi dake Kunduga, Jihar Barno.

Ita dai Kasuwan Kifi, gari ne da ake hadahadar kasuwanci tun safe har dare.

‘yan kunar bakin waken sun kai harin ne da karfe 8 na daren Juma’a a daidai mutanen na harkokin su.

Kamar yadda kakakin rundunar’yan sandan Jihar Damian Chukwu ya bayyana wa manema Labarai cewa wannan kasuwa ya Kan cika makil da masu soya kosai da matasa masu buga wasanni kamar su ‘Snooker’ da sauran su.

Mutane 18 ne suka rasa rayukan su inda wasu 20 suka samu raunuka dabam dabam.

Share.

game da Author