Dalilin da ya sa dimokradiyya ba ta samar wa ‘yan Afrika ‘yanci -Jega

0

Tsohon Shugaba Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana rashin jin dadin yadda mulkin dimokradiyya ta kasa samar da kwakwaran ‘yancin al’ummar Afrika.

Ya kuma ce sun kasa fahimtar cewa ingattacen zabe shi ne ginshikin turbar dimokradiyya.

Jega shi ne ya gudanar da zaben 2011 da 2015, ya yi wannan jawabi jiya Juma’a a Abuja yayin da ya halarci taron da cibiyar jaddada dimokradiyya ta shirya, CCC.

“A yau mun lura a nan Afrika duk da cewa an samu nasarar kafa dimokradiiya, amma har yanzu dimokradiyyar nan ba ta samar wa ‘yan Afrika ingantaccen ‘yancin da ya kamata dimokradiyyar ta samar ba.

“Har yanzu mu na fuskantar matsaloli da kalubale masu yawan gaske. Neman kafa dimokradiiya na fama da bacin rai matuka.

“Misali, daya daga cikin shika-shikan dimokradiyya shi ne gudanar da zabe a kai akai. Amma a yawancin kasashen Afrika, ana yi wa lokuta da wa’adin yin zabe jan alewa, ko kuma a tubka masa igiya mai tsawo, a yi ta jan lokaci.”

Jega ya ce a karshe idan ma an gudanar da zaben, za a cewa wadanda aka zaba ba su yi wani tasiri a zukata ko a fannin ingata rayuwar al’ummar da suka zabe su ba.

“Don haka ni ina ganin sahihin zabe shi ne mabudin bude kowace kofar dimokradiyyar da aka kulle.” Inji Jega.

Share.

game da Author