2019: PDP ta tabbatar ta tsaida nagartaccen dan takara –IBB

0

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Bababangida, ya ja kunnen PDP da ta tabbatar ta tsaida dan takara nagari a zaben 2019 mai zuwa.

A cikin wani bayani da kakakin yada labaran PDP, Kola Olegbodiyan ya fitar, ya ce Babangida ya furta haka a Minna, a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin gudanarwar jam’iyyar PDP, a karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar, Uche Secondus.

A yanzu dai PDP na kokarin ganin ta koma kan mulki, tun bayan faduwa zaben da ta yi a 2015.

Jam’iyyar ta ce kokarin gyara da sauye-sauyen da PDP ke yi, zai kara ba jam’iyyar haske da kwarin-guiwar samun nasara a zaben 2019.

“Ina kuma farin cikin ganin cewa duk da rikice-rikicen da suka gudana, ba ku yi watsi da jama’a kun manta da su ba. Ina biye da sha’anin ku. Na bi yadda ku ka maida hankali a Benuwai da Taraba. Kuma na ji jam’iyyar ku ta tura tawaga a jihar Zamfara.

“To kun ga irin wannan zai sa jama’a ba za ta manta da ku ba, domin kun tabbatar musu kuma kun nuna musu kuna tare da su a lokacin da su ke cikin halin kunci da damuwa.”

Tun da farko sai da shugaban jam’iyyar PDP ya bayyana wa Babangida cewa ya zama dole tsoffin shugabannin kasar nan su tashi su hada kai domin a ceto kasar nan sannan a kara ciyar da ita gaba.

Share.

game da Author