Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya Kinsley Moghalu ya bayyana ra’ayin sa na fitowa takarar shugabancin Najeriya a 2019.
Ko da yake Moghalu bai fadi ko a wace jam’iyya zai yi takara ba ya ce ya yanke shawarar yin haka ne bayan shawara da yayi saboda a ceto Najeriya daga matalolin da take fama dashi.
Wasu daga cikin abubuwan da zan gyara a Najeriya sun hada da gyara fannin ilimin Najeriya, Kiwon Lafiya da wutan lantarki.