2019: INEC ta kara bude cibiyoyin yin rajista 10 a Abuja

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta kara bude cibiyoyin aikin rajistar katin zabe, CVR har guda 10 a Abuja, inda a yanzu FCT na da cibiyoyin yin rajista 32 kenan.

Wata jami’ar INEC mai suna Ndidi Okafor ce ta bayyana haka a Abuja, yayin kaddamar da cibiyar yin rajista a Fadar Shugaban Kasa a jiya Laraba.

Okafor ta ce INEC ta kara wa FCT wuraren yin rajista 10 ne domin a samu damar yin rajista sosai kananan hukumomin Abuja shida.

“Lokacin da aka fara aikin rajista a Abuja a ranar 27 Ga Afrilu, 2017, an bude cibiyoyi shida ne kaal a Abuja.

Amma daga baya sai masu ruwa da tsaki a kan harkar su ka nemi a kara yawan wuraren yin rajistar domin jama’a su samu damar yin rajista sosai da sosai.

“Daga nan ne aka kara wurare 16, suka zama 22 kenan. To a yanzu da na ke magana da ku, an kara wurare 10, sun zama wurare 32 kenan a fadin kananan hukumomin FCT shida.

Okafor ta ce an ware wa Karamar Hukumar AMAC wurare tara, Abaji kuma an kara mata biyu, yayin da Karamar Hukumar Bwari aka mata cibiyoyi a Kubwa da Igu.

A Karamar Hukumar Gwagwalada kuma aka kara a Dobi da Unguwar Sarki.

A Kuje kuma an Rubochi da Kwaku, yayin da a Karamar Hukumar Kwali kuma aka kara a Pai da Yebu.

Share.

game da Author