2019: Fara yin zaben ‘yan majalisun tarayya tonon silili ne ga baragurbi cikin su – Yahaya Bello

0

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya since da kiran da ‘yan majalisar tarayya suka yi na a fara yin zaben kujerun su da gwamnoni kafin ayi na shugaban kasa.

Gwamna Yahaya ya bayyana haka ne da yake amsa tambayoyi daga wakilin mu a fadar shugaban kasa.

Yahaya ya ce wasu da yawa daga cikin wadanda ke majalisar tarayya goguwar Buhari ne ya kawo su. Idan ko aka fara yin na su zaka ga halin mutum ne zai kwace shi ba makalewa da farin jinin shugaba Buhari ba, kamar yadda ya faru a 2015.

” Kusan duka mambobin majalisar tarayya da bazar Buhari suka yi rawa a 2015. Ina goyon bayan a fara yin zaben ‘yan majalisun tarayya kamar yadda suma suke so.

” Idan aka yi haka za ku sha mamakaki domin da yawan su ba za su dawo ba. Idan mutum na kirki ne, zai dawo Tabbas, amma, duk ‘yan kwashi-kwaraf ba za su dawo ba domin dama goguwar Buhari ne ya kai su can.

” Kuma bari in tabbatar muku cewa Buhari ne zai lashe zabe a kasar nan a 2019. Domin ya yi abin da ya cancanci sake rike Najeriya.

Ko da yake majalisar tarayya duk su biyun sun amince da haka, kudirin na gaban shugaban kasa domin rattaba mata hannu ta zama doka.

Game da korafe-korafen da ake yi daga jihar sa kan irin salon mulkin sa, Yahaya ya  ce adawa ce kawai, amma ko a Jihar sa mutane da talakawa sun shaida da abin da suke yi sannan suna yabawa.

Share.

game da Author