2019: Dalilan da ya sa ba zan yi takara, Buhari na so ba – Kingibe

0

Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Baba Gana Kingibe ya yi tir da wadanda suke lika fastan hotunan sa a garuruwan Najeriya wai yana takaran shugabancin Najeriya.

A wata sanarwa da Kingibe ya fitar, ya bayyana cewa ba da yawun sa ba ne ake lika wadannan fasta na sa , sannan bai yi magana da wasu don haka ba.

Kingibe ya kara da cewa ba zai taba yin takara, Buhari na takara ba. “ Ina tare da Buhari kuma idan ya na takara, ni ba zan yi takara ba. Wadannan fasta da ake ta likawa ba da yawuna bane aka lika su.

” Ina tare da Buhari 100 bisa 100. Abin da Buhari yake yi wa kasa Najeriya, ayyuka ne da zai kai Najeriya ga ci.”

Share.

game da Author