2019: A shirye na ke na maye gurbin Buhari – Jonah Jang

0

Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa, Jonah Jang, ya bayyana cewa a shirye ya ke da ya maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari, idan har “jama’ar Najeriya na bukatar canja kasar nan zuwa kasaitacciya.”

Duk da dai cewa har yau Buhari bai bayyana niyyar sa ta tsayawa takara ba, ana sa ran zai tsaya takara a karo na biyu, a karkashin jam’iyyar APC.

Sanata Jang dai dan jam’iyyar adawa, PDP ne, wanda tuni kwamitin da gwamnan da ya gaje shi, Solomom Lalong ya kafa na bincike, ya samu Jang da makarraban sa sun yi rub-da-ciki da miliyoyin kudade.

Jang ya kuma ki amsa gayyatar da kwamitin binciken ya yi masa, amma kuma ya karyata cewa ya yi almubazzaranci a lokacin da ya na gwamna.

Jiya Lahadi kuma Jang ya ce shawarar da tsoffin shugabannin kasar nan, Olusegun Obasanjo da Ibrahim Babangida su ka bai wa Buhari cewa kada ya sake tsayawa takara tunda bai tabuka komai ba, to ta yi daidai.

Sanatan ya yi wannan bayani ne a wata tattanawa da ya yi da manema labarai a gidan sa da ke Du, cikin karamar hukumar Jos ta Kudu, a ranar Lahadi.

Baya ga kara nanata furucin da ya yi kwana biyu baya, da ya ce zama wakili a majalisar dattawa ba na matasa ba ne, sai dattawan, Jang ya kuma dora alhakin kashe-kashen da ake yi da Fulani makiyaya a kan gwamnati ko shugabannin da ke mulki a yanzu.

Da ya ke magana a kan rashin jituwar sa da gwamna Lalong wanda ya gaje shi, sai Jang ya ce “Da farko ni a shirye na ke da na taimaka masa yadda zai ji dadi da saukin mulkin jihar Filato, amma har yau bai karbi tayin da na ke yi masa na mu hadu mu tattauna ba.

“To ta yaya ku ke so zan taimaka ga ci gaban jihar Filato? Don haka ni ba zan iya gane ya yi aiki ko bai yi ba.

Mutanen jihar Filato su ne za su iya dora shi kan sikeli su auna nauyin ci gaba da nasarorin da ya samar a jihar.”

Baya ga cewa bai goyi bayan a gina wa Fulani makiyaya wuraren da za a killace su domin su yi kiwon shanun su ba, Jang ya nanata cewa a shirye ya ke ya fito ya bayar da gudummawar sa wajen shugabancin Najeriya a duk lokacin da ubangiji ya yi masa isharar fitowa takara.

Share.

game da Author