ZAZZABIN LASSA: Rashin mai da hankali ne kan sa likitoci kamuwa da cutar

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa rashin yin la’akari wajen kula da wadanda suka kamu da cutar zazzabin Lassa da likitoci ke yi na daya daga cikin dalilan da ya sa aka samu karin yadawar cutar a tsakanin ma’aikatan kiwon lafiya a shekarar nan.

Ya fadi haka ne a lokacin da ya kai wa gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ziyara a Abakaliki inda ya nuna rashin jin dadin yadda cutar ta yi wa mutane illa a jihar.

Ya ce kamata ya yi likitocin su dunga amfani da kayan aiki na kariya yayin da suke kula da wadanda suka kamu da cutar gudun kada su kamu da shi suma.

Share.

game da Author