ZAZZABIN LASSA: Mutane 21 ne suka rasu cikin 77 da suka kamu da cutar a Najeriya

0

Shugaban hukumar hana yaduwar cutuka na kasa NCDC Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa cutar zazzabin Lassa ta yi ajalin mutane 21 daga cikin 77 da aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya.

Ihekweazu ya kara da cewa cikin mutane 77 din da aka tabbatar na dauke da cutar 10 daga cikinsu ma’aikatan kiwon lafiya ne.

Ya ce koda yake shugaban asibitin Irrua dake jihar Edo Sylvanus Okogbeni ya tabbatar musu cewa cikin ma’aikata 10 da suka kamu da cutar an sallami biyu ranar Litini amma bullowar cutar ya tsorata da kuma fusatar da wasu masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya a kasar nan.

Bayan haka Ihekweazu ya ce hukumar sa ta raba magungunan kawar da cutar wanda ake kira da ‘Ribavirin drugs’ a yankunan da cutar ta bullo sannan za su hada hannu da shugabanin asibitoci domin wayar da kan mutane kan hanyoyin da za su bi don guje wa kamuwa da cutar.

Share.

game da Author