ZAZZABIN LASSA: Likitoci a Ebonyi sun roki gwamnati da su kawo musu dauki

0

Likitoci a jihar Ebonyi sun gudanar da tattaki zuwa fadar gwamnatin jihar don nuna rashin jin dadin su game da mutuwar abokanan aikin su uku sanadiyyar kamuwa da cutar zazzabin Lassa.

Likitocin sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa a yanzu haka wani abokin aikin su na nan a kwance ‘rai kwa-kwai mutu kwa-kwai’ a asibitin Irruwa, jihar Edo.

Likitocin sun ce sun yi wannan tattaki ne domin yi wa gwamnati barazana da nuna fushin su kan watsi da akayi da su da kuma rashin inganta fannin lafiya a jihar.

Sun koka cewa duk shekara sai irin haka ya sami daya daga cikin ma’aikatan su wanda sakaci ne na gwamnatin a jihar.

Share.

game da Author