Kwaminshinan ilimi na jihar Ebonyi John Eke ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yanke shawarar rufe duka makarantun jihar ne saboda kare ‘yan makaranta daka kamuwa da cutar zazzabin Lassa da ya bullo a jihar.
Eke ya sanar da haka ne ranar Alhamis da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Abakaliki.
” Bada umurnin rufe makarantun ya zama mana dole musamman yadda asibitocin jihar a jiya Laraba ta sanar da mu cewa wata mata wanda ya’yan ta ke karatu a daydaga cikin makarantun jihar ta kamu da wannan cuta, wanda ganin haka ya sa muka ce lallai ya kamata mu rufe makarntun gudun kad cutar ya yadu.”
a
Yanzu halin da ake ciki dai duk makarantun jihar na kulle, sannan gwamnati tayi kira ga mutanen jihar da su maida wajen tsaftace muhallin su domin gujewa kamuwa da wannan cuta.
Kwamishinan ya ce ba wai cutar ta gagari gwamantin jihar bane, ta yi haka ne domin ta tabbatar da ta samar da isasshen kariyar da ya kamata musamman ga yan makaranta kafin a bude su.
Bayan haka kuma an canza wa marasa lafiya wurin jinya a asibitin gwamnati dake jihar domin samar musu da kariya.
Idan ba a manta ba a cikin wannan makon ne likitoci a jihar suka gudanar da tattaki zuwa fadar gwamnatin jihar don nuna rashin jin dadin su game da mutuwar abokanan aikin su uku sanadiyyar kamuwa da cutar zazzabin Lassa.
Likitocin sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa a yanzu haka wani abokin aikin su na nan a kwance ‘rai kwa-kwai mutu kwa-kwai’ a asibitin Irruwa, jihar Edo.
Likitocin sun ce sun yi wannan tattaki ne domin yi wa gwamnati barazana da nuna fushin su kan watsi da akayi da su da kuma rashin inganta fannin lafiya a jihar.
Sun koka cewa duk shekara sai irin haka ya sami daya daga cikin ma’aikatan su wanda sakaci ne na gwamnatin a jihar.
Bayan haka kuma babban darektan asibitin gwamnati dake jihar NAsarawa Joshua-Ndom ya bayyana cewa suna gwada jini wasu mutane uku da ake zargin sun kamo da cutar zazzabin Lassa a jihar.,
Joshua ya ce gwamnatin jihar na iya kokarin ta don ganin cutar bai yadu a jihar ba sannan ya yi kira ga mutanen jihar da su kwantar da hankalin su.