ZAZZABIN LASSA: An yi kira da a rage shan garin kwaki

0

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya gargadi mutanen jihar da su rage shan garin kwaki saboda bullowar cutar zazzabin Lassa a jihar.

Maitaimaka masa kan harkokin yada labarai Sam Onwuemeodo ya sanar da haka wa PREMIUM TIMES inda ya kara da cewa cutar ta yi ajalin mutane uku sannan an sami tabbacin cewa mutane bakwai na dauke da cutar a asibitin dake Orlu da kuma sauran bangarorin jihar.

” Rage shan garin kwaki ya zama dole musamman yadda ita ba dafata ake yi ba sannan babu wanda zai iya ganewa ko bera ya yi fitsari ko kuma yayi birgima a ciki.”

Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar da ma’aikatar kiwon lafiya na iya kokarin su wajen ganin sun dakile ya duwar cutar.

Ganin haka ne yasa gwamnati tayi kira da a daina taruwa wuri daya, a rage shan hannu wajen gaisuwa sannan a rika tsaftace muhalli da kuma abincin da za a ci.

Share.

game da Author