Gwamnatin jihar Ebonyi ta bude makarantun Jihar bayan kulle su da tayi don guje wa yaduwar cutar zazzabin lassa da ya bullo a jihar a makon da ya gabata.
Idan ba a manta ba a ranar 18 ga watan Janairu gwamnatin jihar ta bada umurnin a rufe wadannan makarantu saboda gujewa yaduwar cutar a makarantu.
Kwamishinan ilimi na jihar John Eke ya ce sun bude makarantun ne ganin cewa komai ya lafa babu sanarwan kamuwa da cutar sannan gwamnati ta hada kawance da hukumar NCDC da WHO don ci gaba da wayar da kan mutane kan hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
Discussion about this post