Zaharadden, Zango, Maryam sun burge a fim din Dawo Dawo

0

Idan har kana bukatan kallon wani shirin Kannywood da yake da ma’ana da zai saka ciki dimuwa da nazarin gaske, toh, ka kalli fim din Dawo Dawo.

” Ni dai na kalli fim, a shekarar nan, ban taba ganin fim din da ya burgeni irin Dawo Dawo ba. ” Hassana Dalhat.

Adam Zango, Maryam Jos, Aisha Tsamiya, Tijjani Faraga, Zaharadden Sani duk sun nuna hazakar su a wannan fim.

Na dade Ina kallon fim din Kannywood, musamman a shekarar da ta gabata, ban kalli fim din da ya natsar dani kamar Dawo Dawo ba.

Ya karantar da yadda ‘ya’ya ya kamata suyi biyayya ga iyayen su.

Ya nuna yadda so ke iya zama dalili kan komai a rayuwa.

Ya karantar da kamala da yadda hukuncin Allah idan yazo babu abinda ke iya dakatar da shi.

Ya nuna makircin mace karara.

Zabin ‘yan wasan da suka fito a fim din kawai ya burge masu Kallo. Ko wani dan wasa ya yi daidai da a inda aka sa shi.

NA DAWO

Ci gaban shirin Dawo Dawo, ya burge domin darektan fim din bai kauce layi ba. Ya tsaya a yadda ya faro shirin tun a farko.

(Zaharadden Sani) wanda shine gogan a shirin, ya yi nadaman abin da ya aikata, sannan ya nemi ya ga dansa da ake rike masa a gidan (Adam Zango.)

Bayan da na gama kallon fim din, anawa ganin babu dalili a yi masa ci gaba. Labarin ya zo karshe, sai dai muna jira mu gani.

Ali Gumzak Sak ne yayi darektin.

Share.

game da Author