Za mu sa kafar wando daya da miyagun mutane a Kaduna – Kwamishinan ‘yan sanda

0

Sabon kwamishinan ‘yan sandar jihar Kaduna Austin Iwar ya lashi takobin ganin an kawo karshen ayyukan ta’addanci da ya hada da sace-sacen mutane da miyagun ayyuka a jihar.

Ya sanar da haka ne wa manema labarai a Kaduna ranar Alhamis inda ya kara da cewa matakan da za su yi amfani dasu don haka za su kunshi wayar da kan mutane game da hanyoyin da za su iya bi don kare kan su daga fada wa irin wannan miyagun mutane.

Ya ce wannan dabarun da za suyi mafani da su zai ta taimaka wajen saukaka aiyukkan ‘yan sanda a jihar musamman ganin cewa ba ko Ina bane ‘yan sandan za su iya zuwa na take.

Daga karshe ya bayyana cewa rundunar sa za ta tsananta hukunci ga duk wanda aka kama da laifi. Wannan karon babu wasa, kowa ya shiga taitayin sa.

Share.

game da Author