Kungiyar sarrafa magunguna ta Najeriya PCN tare da hadin guiwar wasu kungiyoyi na kokarin tsaro hanyoyin hana amfani da maganin tari mai dauke da sinadarin ‘Codeine’ domin kawar da matsalar shan kwayoyi barkatai da musamman matasa ke yi.
A tsokacin da ya yi jami’in PCN Elijah Mohammed ya ce an yi maganin ‘Codeine’ don kawar da tari ko kuma ciwon jiki amma sai ga shi yanzu mutane na amfani da shi don suyi maye.
Ya ce wayar da kan mutane kan illolin dake tattare da amfani da irin wadannan magunguna na daga cikin hanyoyin da suka dauka domin yaki da shan kwayoyi a kasar nan.
Discussion about this post