Yusuf Buhari ya samu sauki, inji Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa Yusuf Buhari, dan Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya ji ciwo sakamakon hadadrin babur din da ya yi da babur din tsere, ya samu sauki.

Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa ana ma shirin sallamar Yusuf daga Cedar Crest Hospital, inda aka kwantar da shi a Abuja, tun a ranar da ya yi hadarin a ranar 26 Ga Disamba, 2017, a Gwarimpa, Abuja.

Shi ma Adesina, sai ya kara da ruwaito wani jawabi da Babban Daraktan asibitin, Felix Ogedegbe ya ruwaito.

Jawabin dai ya yi nuni da yadda aka samu kwararrun likitocin asibitin su ka dira kan yi wa Yusuf aikin tiyatar kwakwalta da kuma masu dorin gocewa da targade.

Ogedegbe ya ce tun bayan aikin da aka yi masa, ya rika samun sauki a cikin gaggawa. Sannan kuma ya danganta saukin da Yusuf ya samu da sauri da irin kwararrun likitoci da kayan aikin da asibitin ya ke da shi.

Sai dai kuma ya yi tir da rudun da aka rika yadawa a soshiyal midiya cewa Yusuf ya yi hadarin ne tare da wani abokin sa. Shugaban asibitin ya ce shi kadai ne ya yi hadari, ba tare ya ke da kowa ba.

Sannan kuma ya ce karairayi ne kawai da shirme na soki-burutsu da aka rika yada cewa wai Aisha Buhari ta yanke jiki ta fadi saboda firgita da halin da dan ta Yusuf ya tsinci kan sa.

Ya kara da cewa duk karya ce, ba ta nuna firgita ba, ballantana har ta fadi har kuma a kwantar da ita ma a asibitin na Cedar Crest Hospitals a Abuja.

Ya ce tun da farko asibitin yak i maida hankali ne kan soki-burutsun da akarika yadawa, saboda su aikin da ke gaban su ne ya fi damun su, ba maida martanin surutai marasa ma’ana da aka rika yadawa a lokacin ba.

A karshe ya gode wa Ministan Lafiya da sauran ‘yan Nijeriya.

Share.

game da Author