Yarbawan Jihar Kogi sun ki amincewa a gina wuraren kiwon shanu a jihar

0

Yarbawan jihar Kogi sun ki amincewa a gina dangwalin shanu, inda za a killace makiyaya da shanun su a wuri daya ga cikin kananan hukumomi shida da Yarbawan suka yi kakagida a jihar.

Bayan tashi daga wani babban taron su na gaggawa na kungiyar ci gaban Okun, a garin Kabba, a ranar Asabar da ta gabata, mutanen sun ce batun da Ministan Gona Audu Ogbeh ya yi na kokarin kafa dangwalin shanu a jihohin kasar nan, bai dace ba, kuma rashin adalci ne.

Yarabawan jinsin Okun, wadanda ke cikin kananan hukumomin Kabba-Bunu, Ijumu, Lokoja, Yagba ta Yamma, Yagba ta Gabas da kuma Mopamuro, sun ce duk wani yunkurin a kamfaci kasar noman su ta gado a gina dangwali don kawai a dadada wa Fulani makiyaya hanyar kiwon su, to an tsokano-tsuliyar dodo ne tabbas.

Sun ce dangwalin shanu hatsari ne, don haka maganar kakkafa dangwalin shanu zai janyo wa kasar nan bala’i.

Sun bayyana haka ne a wata takardar bayan taron da suka fitar bayan kammala taron na su, su ka kuma kara jaddada cewa ba za su amince a gina wa Fulani dangwali ba.

Jihar Kogi na daya daga cikin jihohin da suka amince a gina dangwalin shanu a jihar, wato ‘colony’, inda har gwamna Yahaya Bello ya yi wa sauran Fulanin da ke fuskantar matsi ko tsangwama a wasu jihohi cewa su tattaro ya-na-su-ya-na-su, su koma jihar Kogi da zama.

Yahaya Bello ya kuma bada umarnin cewa duk wadanda suka koma jihar, to a gaggauta yi musu takardar zama ‘yan kasa a jihar.

To sai dai kuma takardar da Yarbawan suka fitar bayan taron su, wadda Shugaban su na Kasa, Femi Mokikan da Sakataren su na Kasa, Ayo Abereoran su ka sa wa hannu, sun yi fatali da tayin da gwamnati ta yi wa Fulani makiyaya, na gina musu dangwali da kuma maida su ‘yan asalin jihar Kogi.

Share.

game da Author