‘Yar Chibok da a ka ceto na Asibiti ana duba ta tare da wata ‘yar shekara 14

0

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto wata yar makarantar sakandare na Chibok daga cikin sauran da suka rage a hannun Boko Haram.

Idan ba a manta ba ‘yan Boko Haram sun sace ‘yan mata sama da 200 a makaratan sakandare dake Chibok jihar Borno a watan Afirilu 2014.

Bayanai da suka fito daga rundunar sojin sun ce a yau Alhamis dakarun ‘Operation Lafiya Dole’ da suke aiki a kauyen Pulka suka ceto wannan yarinya mai suna Salomi Pagu.

A yanzu haka Salomi Pagu tare da wata yarinya dake da goyo mai suna Jamila Adams ‘yar shekara 14 da aka ceto su tare na hannun sojojin sannan suna samun kulan da suke bukata a asibiti.

Share.

game da Author