Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu rahoton aikata fyade a jihar har sau 210 a cikin 2017.
Kakakin rundunar, Isa Gambo ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a Katsina cewa an kama mutane har 275 da ake zargi da fyade a cikin 2017.
Gambo ya kara da cewa yanzu haka akwai kararraki har 2017 a gaban alkalai da ke kotuna daban-daban, masu alaka da aikata fyade. Ya ce sauran uku kuma ana kan binciken su.
Kakakin ya ce a cikin 2017, an kama wadanda ake zargi da aikaya fashi da makami har mutum 320, yayin da aka samu rahotannin fashi da makami har a wurare 204 duk a cikin 2017.
Gambo ya ci gaba da cewa ana kan gurfanar da rahotannin fashi har 155, yayin da ake kan binciken sauran.
An kuma samu rahotannin kisa a wurare 150, inda aka kama mutane 319 dangane da hannu a zargin kisa duk a cikin 2017.
Da ya ke magana a kan satar shanu kuwa, Gambo ya ce an kwato shanu 313, tumaki 24 daga barayin shanu 29 a cikin 2017.
Ya kuma yi magana a kan yawan kudade da bindigogin da aka samu a hannun ‘yan fashi da makami. Sannan kuma ya koka da matsalar kayan aiki.
Discussion about this post