’Yan sanda sun tarwatsa zanga-zangar ’yan Shi’a harbi a Abuja a karo na biyu

0

’Yan sandan Najeriya sun yi harbi sama, sannan su ka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa zanga-zangar ‘yan Shi’a yau Alhamis a Abuja.

Daruruwan su ne su ka fito kan titinan Abuja, su ka fara zanga-zanga, tun daga Garki Area 10 su ka darkaki Area 1.

Sai dai kuma ’yan sanda sun tare su daidai mahadar titin Mashood Abiola a Area 2 inda su ka hana wucewa.

Masu zanga-zangar sun yi kumumuwar matsawa gaba, amma sai jami’an tsaron su ka fara surfa harbin bindigogi a sama, tare da antaya musu barkonon tsohuwa.

Hakan ya sa an tarwatse, tare da haifar da rudani ga masu saye da sayarwa, mazauna unguwannin da kuma masu zirga-zirga a kan motoci, inda kowa ya yi ta kan sa.

Masu zanga-zangar dai sun shiga rana ta biyu kenan su na zanga-zangar sai-Baba-ta-gani a Abuja, da nufin a sako jagoran su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da ke tsare shekaru biyu kenan.

Tuni dai masu zanga-zangar ke ta watsa sanarwa a soshiyal midiya cewa sun a ci gaba da gaggayatar jama’a a fito gobe Juma’a a rana ta uku, domin a ci gaba da zanga-zanga, har sai an saki shugaban na su.

Share.

game da Author