‘Yan sanda sun hana Kwankwaso shirya taro a Kano

0

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta shawarci Sanata Rabi’u Kwankwaso da ya soke gagarimin taron da ya shirya yi a ziyarar da ya yi niyyar kai wa Kano, a nar 30 Ga Janairu, 2018.

Rundunar ta ce sun bayar da wannan shawara ce domin hakan ne zai sa a kauce wa rikici a jihar.

Rundunar ta kara bayyana cewa a sani, jami’an tsaro za su yi aikin su na hana barkewar tarzoma idan har rikici ya nemi barkewa.

Wannan ziyara da Kwankwaso ya yi niyyar kai wa Kano dai ta haifar da maganganu da yawa, bangarorin Kwankwaso da na Gwamna Abdullahi Ganduje ke zargin juna da kokarin haddasa fitina.

Kwamishinan ’Yan sanda Rabi’u Yusuf, ya ce jami’an tsaro ba za su zuba ido su ka ana karya doka haka kawai ba tare da sun kai jiki sun kwantar da tarzoma ba.

“Mun samu kwakkwaran rahoton cewa akwai tsananin tsoro a zukatan jama’a, ganin yadda garin ya rigaya ya dau zafi.

Dalili kenan muke shawartar Kwankwaso da ya soke wannan ziyara da zai kawo.” Inji Kwamishinan ’Yan sanda Yusuf.

“Duk da cewa Sanata Kwankwaso kamar sauran jama’a na da ’yancin yin tarukan sa kamar yadda tsarin mulkin kasar nan ya tanadar, to amma rahotanni sun a cike da nuna cewa komai zai iya faruwa a yayin wannan ziyara.”

A kan haka ne ya ce ya kamata a soke ziyarar, domin a wanzan da dauwamammen zaman lafiya a Kano, gudun kada batagari su yi amfani da ziyarar su hargitsa Kano.

Ya kara da cewa sai jiya Alhamis, 25 Ga Janairu ya samu wasikar sanar da ziyarar da Kwankwaso zai kai Kano, duk da cewa tun a ranar 16 Ga Janairu aka aika masa da wasikar.

Share.

game da Author